Kungiyar Kare Muradun Musulman Najeriya (MURIC), ta garga?i masu shirya zanga-zanga cewa zanga-zangar fushin fama da yunwar da suke shirin tsunduma za ta iya haifar da gagarimar yunwar da ba a ta?a fuskanta ba.
?ungiyar ta ja hankalin matasa cewa su bi a hankali, su yi ha?uri, sannan kuma su amince a zauna teburin sulhu.
Wannan matsayi da MURIC ta ?auka ta fitar da shi ne a ranar Talata, daga bakin Babban Daraktan Ishaq Akintola.
“Matasan Najeriya wa?anda manyan ‘yan adawa ke ?aukar nauyi sun shirya fita zanga-zangar nuna fushin tsadar abinci da yunwa, nan da sa’o’i 48,” inji Farfesan.
“Kasar nan baki ?aya ta ?au zafi, ta ?au caji, to babban abin da tsoron shi ne abin da ka iya biyo baya. Najeriya za ta hau kan sira?in da za ta ri?a tangal-tangal, har yunwa ta afko wadda ba a ta?a fuskantar irin ta ba a tarihin ?asar nan.
“Duk da cewa mun yi magana cewa a yi taka-tsantsan, duk da haka mun sake ganin cewa akwai bu?atar mu ?ara jawo hankalin matasa tare da fito da matsayar mu kan wannan zanga-zanga mai ?aratowa.
“Muna kira da jaddada garga?i ?arara cewa wannan zanga-zanga da suke kira zanga-zangar yunwa, za ta iya kasancewa kamar gayyato wa kan mu gagarimar yunwa ce wadda ba a ta?a fuskantar irin ta ba a tarihin ?asar nan.”
MURIC ta ce a gaskiya rashin adalci ne da kuma gaggawa da har za a ?ora laifuka n matsalolin da ?asar nan ta shiga shekara da shekaru a kan gwamnatin da ba ta fi shekara ?aya kan mulki ba.
MURIC ta jawo Hadisin Annabi SAW, yake cewa, “Farkon fushi hauka ne, sannan kuma ?arshen sa yin da-na-sani.”
A ?arshe MURIC ta buga misali da irin mummunar ?arnar da aka yi a Kenya, wadda yanzu ‘yan ?asar ke da-na-sanin irin gagarimar ?arnar.