Kungiyar Kare Muradun Musulman Najeriya (MURIC), ta gargaɗi masu shirya zanga-zanga cewa zanga-zangar fushin fama da yunwar da suke shirin tsunduma za ta iya haifar da gagarimar yunwar da ba a taɓa fuskanta ba.
Ƙungiyar ta ja hankalin matasa cewa su bi a hankali, su yi haƙuri, sannan kuma su amince a zauna teburin sulhu.
Wannan matsayi da MURIC ta ɗauka ta fitar da shi ne a ranar Talata, daga bakin Babban Daraktan Ishaq Akintola.
“Matasan Najeriya waɗanda manyan ‘yan adawa ke ɗaukar nauyi sun shirya fita zanga-zangar nuna fushin tsadar abinci da yunwa, nan da sa’o’i 48,” inji Farfesan.
“Kasar nan baki ɗaya ta ɗau zafi, ta ɗau caji, to babban abin da tsoron shi ne abin da ka iya biyo baya. Najeriya za ta hau kan siraɗin da za ta riƙa tangal-tangal, har yunwa ta afko wadda ba a taɓa fuskantar irin ta ba a tarihin ƙasar nan.
“Duk da cewa mun yi magana cewa a yi taka-tsantsan, duk da haka mun sake ganin cewa akwai buƙatar mu ƙara jawo hankalin matasa tare da fito da matsayar mu kan wannan zanga-zanga mai ƙaratowa.
“Muna kira da jaddada gargaɗi ƙarara cewa wannan zanga-zanga da suke kira zanga-zangar yunwa, za ta iya kasancewa kamar gayyato wa kan mu gagarimar yunwa ce wadda ba a taɓa fuskantar irin ta ba a tarihin ƙasar nan.”
MURIC ta ce a gaskiya rashin adalci ne da kuma gaggawa da har za a ɗora laifuka n matsalolin da ƙasar nan ta shiga shekara da shekaru a kan gwamnatin da ba ta fi shekara ɗaya kan mulki ba.
MURIC ta jawo Hadisin Annabi SAW, yake cewa, “Farkon fushi hauka ne, sannan kuma ƙarshen sa yin da-na-sani.”
A ƙarshe MURIC ta buga misali da irin mummunar ɓarnar da aka yi a Kenya, wadda yanzu ‘yan ƙasar ke da-na-sanin irin gagarimar ɓarnar.