Shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 da Abuja sun ci alwashin cewa ba za su zuba ido su na kallo wasu batagari su kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba da sunan zanga-zanga.
Sakataren kungiyar ciyamonin APC na ƙasa, wanda kuma shine Ciyaman din jam’iyyar a Cross River, Alphonsus Ogar Eba a taron manema labarai a shelkwatar jam’iyyar ta ƙasa a yau Litinin ya ce zanga-zangar ta kwanaki goma wani shiri ne na kifar da gwamnatin Tinubu.
Ciyamonin jam’iyyar sun yi gargaɗin cewa duk wanda ya gaje da zanga-zangar ya tada fitina to fa ba zai ga da kyau ba.
Ta kuma ci alwashin tattara kan shugabannin jam’iyyar tun daga mazaba har zuwa matakin niha daga ranar 29 ga Yuli zuwa 11 ga Agusta don su rika yada muhimman ayyukan alheri da Tinubu yayi daga hawan sa zuwa yanzu.
“Mu na kira ga ƴan ƙasa masu kishi da kada su bari a hilace su zuwa shiga zanga-zanga, wacce ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar da mu ke ciki yanzu.
“Haka mu na kira ga jami’an tsaro da su kawo rahoton suka wani wanda ya ke yunkurin tada zaune tsaye,” in ji Sakataren.