Zan Tsaftace Harkokin Finafinai A Najeriya – Sarki Ali Nuhu

IMG 20240317 WA0069

Shugaban huukumar fina-finai ta Najeriya (NFC), Sarki Ali Nuhu ya yi alkawarin inganta harkar fina-finai domin taimakawa tattalin arzikin kasa ya bunkasa cikin sauri.

Ali Nuhu ya yi wannan alkawarin ne a wurin bikin miƙa masa ragamar hukumar a Jos, babban birnin jihar Filato, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jarumin na masana’antar Kannywood ya zama shi ne manajan darakta na hukumar fina-finai ta Najeriya (NFC) na bakwai a tarihi. Yayin da ya kama aiki a matsayin MD na NFC, Ali Nuhu ya tabbatar wa mahalarta taron cewa ya shirya tsaf domin aiki tuƙuru da nufin inganta aikin hukumar.

Yabayyana kwarin gwiwar cewa zai yi amfani da dimbin kwarewarsa wajen bunkasa masana’antun fina-finai daban-daban da ake da su a Najeriya.

Ali Nuhu ya kuma jaddada tsammanin da gwamnatin tarayya, masu shirya fina-finai, masu ruwa da tsaki, da al’ummar Nijeriya ke yi wa hukumar, inda ya bayyana muhimmiyar rawar da take takawa.

“Zan jagoranci samar da kayan aikin shirin fina-finai na zamani domin kawo ci gaba da kuma tabbatar da cewa masana’antun mu sun shiga ana gogayya da su a duniya.”

“Zan daga darajar fina-finan Najeriya a gida da waje. Na shirya dabarun hadin gwiwa kamfanoni masu zaman kansu, masu ruwa da tsaki na kasa da kasa da jama’a akan inganta ayyukan mu.”

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply