Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce sanya sabbin dabarun fasahar sadarwar zamani na digital a dukkanin ayyukan gwamnati babban cigaba ne wajan nasara ga yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati.
Ministan ya yi wannan tsokaci ne a taron karawa juna sani na kasa kan yaki da cin hanci da rashawa wanda Code of Conduct Bureau, (CCB) ta shirya tare da tallafin Babban Bankin Najeriya mai taken: “Code of Conduct Bureau: Fighting Corruption For Socio-Economic Development in Najeriya” da aka gudanar a babban Birnin Tarayya Abuja.
Minista Pantami ya samu wakilcin shugaban hukumar bunkasa Fasahar Sadarwar zamani ta Kasa (NITDA), Kashif Inuwa, a yayin taron karawa juna sani ya yi kira da a sanya sabbin dabarun fasahar sadarwar zamani na digital a dukkanin ayyukan gwamnati don kawo karshen matsalar cin hanci da rashawa da ta addabi kasar.
Ya ce, “A lokacin da ma’aikatan gwamnati suke gudanar da ayyukan su, da tafiyar da dukkanin aikace-aikacen su babu wanda zai mallaki karfin ikon boye wani abu, babu wanda zai yi komai yadda ya ga dama saboda lokacin da ake aiwatar da aikin kai tsaye, komai zai kasance a bude kuma bayyane kowa yana gani.
Wannan zai karawa dimokradiyya karshashi wajan gudanar da ayyuka cikin gaskiya, ta yadda za a dinga bayar da lissafi, ana adana bayanai kuma ana iya bincikarsa a duk lokacin da ake bukata”.
Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki ta Tarayya na yin abubuwa da yawa don dakile duk wata zamba ta cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikata wadanda hakan ke kawo cikas ga cigaban kasar.
“Akwai bukatar a cigaba da Kirkirar dabaru da manufofin da za su magance irin wannan aika-aikar na cin hanci da rashawa, Wanda zai samar da hanyoyin ci gaban kasar cikin sauri, in ji shi.
Dakta Pantami ya tabbatar wa wadanda suka shirya taron cewa Ma’aikatarsa za ta basu cikakken goyon baya ga ayyukan Code of Conduct Bureau da nufin magancewa da kuma kawar da ayyukan cin hanci da rashawa a duk fadin kasar, don samar da yanayin da zai ba da gaskiya da rikon amana ga ayyukan gwamnatin.