Zan Rungumi Kowa A Mulkina – Sarki Bamalli

Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya yi jawabi bayan zamansa Sarkin Zazzau. Sabon Sarki ya ce ya na da kyakkyawar dangantaka da Katsinawa da Bareberi

Mai martaba ya yi kira a fawwala lamari ga Ubangiji mai karfin bada mulki

Sabon sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya yi kiran hadin-kai a lokacin da ya yi jawabi, jim kadan da nada shi magajin Shehu Idris.

A wani gajeren bidiyo da ya shigo, an ji Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya na alkawarin cewa zai tafi da kowa a mulkinsa.

Ahmed Nuhu Bamalli ya yi jawabi ne a fadarsa bayan an sanar da nadin shi a matsayin Sarki na 19 a masarautar Zazzau a ranar Laraba, 7 ga Oktoba.

Mai martaba ya bayyana cewa ya na da alaka ta kusa da sauran gidajen Katsinawa da Beriberi.

Ina da alaka mai kyau da duka gidajen Zazzau. Mai martaba ya ce bayan haka, akwai mutuncin juna da ake gani tsakanin gidajen da ke sarauta a kasar.

Mai daki na ta fito ne daga gidan Katsinawa domin diyar Marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris. Kakannina daga bangaren uwa, jinin Bareberi ne

Don haka ban ga abin da zai sa in samu sabani da wadannan gidaje ba. Inji Sarki Bamalli.

Ubangiji ne ya ke bada Sarki, ba kudin mutum ba ne, ko dukiyarsa, ko karfin mulki. Sarkin ya ke fada a wannan gajeren jawabi da ya yi ba da dadewa ba.

Sabon Sarkin ya cigaba da cewa, Idan da wadannan ne su ke bada mulki, da watakila ba mu zo inda mu ke yau ba. Ya ce Allah ne ya ke bada mulki.

Sarkin ya ce ya ji dadi da ya ga gidajen Katsinawa da Barebari sun yi mubaya’a.

Ya ce zai yi kokarin hada-kan mutanen Zazzau a kankanin lokaci

Labarai Makamanta

Leave a Reply