Zan Roki A Yafe Wa Najeriya Bashi Idan Na Zama Shugaban Kasa – Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai nemi a yafewa Najeriya bashin da ke kanta na kasashen waje idan ya gaji Buhari a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin da yake magana kan shirinsa na farfado da tattalin arzikin Najeriya. Ya kuma bayyana cewa, shirinsa na mai da bangarori da dama hannun ‘yan kasuwa zai samarwa ‘yan Najeriya aikin yi.

Atiku ya yi wannan batu ne a wani taron tsoffin daliban makarantar kasuwanci ta Legas da aka gudanar na shekarar 2022, a birnin Ikko na Jihar Legas.

Da yake magana game da halin rikicin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a yanzu, Atiku ya ba da misali da nasarorin da PDP ta samu tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 sadda yake mataimakin shugaban kasa. Mun yi a baya, yanzu ma za mu yi A cewarsa, a wancan lokacin, gwamnatin PDP ta yi nasarar nemawa Najeriya afuwar bashin da ake binta, kana gwamnati ta habaka tattalin arzikin kasar cikin kankanin lokaci ta hanyar hada kai da kamfanoni masu zaman kansu.

“Idan ana magana game da bashin kasar waje, mun yi a baya, zan nemi wadanda suke bin bashin sannan na roki su yafe ko kuma su soke shi kamar yadda muka yi a baya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply