Tsohon Shugaban Hukumar kula da ku?a?en Fansho ta ?asa PRTT Abdulrasheed Maina yace zai iya rasa kafarsa indai ba a bashi damar zuwa asibiti neman magani ba, domin halin da ?afar tashi ke ciki.
Maina yana hannun hukuma akan zargin wawurar naira biliyan biyu na kudin fansho kuma ya tsere ya bar sanata mai wakiiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, a hannun hukuma bayan ya tsaya masa a matsayin mai bashi kariya.
An samu nasarar damkarsa a jamhuriyar Nijar inda ya lallaba ya shige, a ranar 3 ga watan Disamban 2020.
Sannan an dakatar da bayar da belin Maina inda aka sa ya cigaba da zama a gidan gyaran hali har sai an kammala shari’arsa.
A zaman kotu da aka yi ranar Juma’a, lauyan Maina, Sani Katu ya bukaci a bayar da belin Maina saboda halin rashin lafiyar da yake ciki.
A takardar kotu Katu ya ce Maina zai iya rasa kafarsa matukar ba a bashi beli ya nemi lafiya ba.
“Muna bukatar alkali ya taimaka ya bayar da belin Maina sakamakon hali na rashin lafiya da yake ciki, don hakan babban hatsari ne ga rayuwarsa.”
Saidai a nashi bangaren Lauyan Hukumar EFCC Mohammed Abubakar, ya nuna rashin amincewarsa akan bayar da belin.
“Idan aka duba yadda aka bashi beli a karo na farko kuma ya bayar da kunya, ba abin amincewa bane,” a cewar Abubakar.
“Maina yana son nuna cewa likitocin Najeriya basu da kayan aiki da kwarewar da zasu iya kulawa da lafiyarsa. Tabbas akwai kwararrun likitoci a gidan gyara hali.”
Alkali Okon Abang, ya dakatar da neman belin har sai ranar 25 ga watan Fabrairu.