Zan Gina Arewa Da Arzikin Man Da Aka Samu Daga Bauchi – Peter Obi

Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar LP, Mr. Peter Obi, ranar Alhamis, ya tabbatarwa da alummar Jihar Bauchi cewa za ayi amfani da danyen man fetur din aka samu a jihar don ciyar da jihar da kuma yankin Arewa gaba.

Ya yi alkawarin ne a yakin neman zaben jam’iyyar da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa a Bauchi, babban birni Jihar a ranar Alhamis.

”Mun san abin da yake faruwa a Bauchi a halin yanzu. Muna son yin amfani da danyen man da aka hako don cigaban Bauchi, da kuma baku ayyukan yi. Zamu tabbatar anyi amfani dashi don cigaban Bauchi, da cigaban Arewa, don tabbatar da komai yana aiki bawai mutum daya ya sace kudin yabar kowa a cikin yunwa ba.

”Ku fita ranar 25 (Fabrairu), ku zabi jam’iyyar Labour, ku nemi LP ku kuma zabi LP, anan za ku ga sabuwar Najeriya.”

Ya bayyana cewa a duk lokacin da yake Bauchi, yana tuna masa lokacin da Najeriya take a matsayin kasa daya mai cike da zaman lafiya jihar ta fitar da daya daga cikin shugabannin da suka sanya kasar alfahari a faɗin duniya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply