Zan Cika Alkawurran Da Na Yi Tun Na 2015 – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa ƴan Najeriya cewa, zai cigaba da cika alƙawuran da ya ɗaukar musu tun daga shekarar 2015.

Shugaban ya bayyana haka ne a fadarsa a ranar Juma’a, bayan da ya karɓi baƙuncin wata ƙungiyar dake goyon bayansa wadda ta wallafa wani littafi akan nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Zan Yi Shugaban ya kuma godewa ƙungiyar da ta saka kuɗinta ta shiga saƙo da lungu dan gano ayyukansa ta haɗasu a wannan littafi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply