Shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC AbdulRasheed Bawa ya ce ya daukaka kara dangane da hukuncin da wata kotun birnin tarayya ta yanke masa ranar Talata a Abuja.
Kotun yanke hukuncin tura shi gidan yari sakamakon kama shi da laifin raina umarnin kotu.
Tun da farko dai kotun ta umarci shugaban da ya mayar da wasu kudi da suka kai naira miliyan 40 da wata motar alfama da hukumar ta karba daga wani mutum da ta zarga da laifin rashawa.
Shugaban EFCCn ya ce shi a karan kansa bai yi watsi da umarnin kotun ba a matsayinsa na shugaban hukumar, ballantana ya fuskanci fushin kotu, saboda a saninsa kotun ta bayar da umarnin ne tun a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018.
Wato shekara uku kenan kafin ya zama shugaban hukumar ta EFCC, zamanin shugabancin Ibrahim Magu dan haka ba shi aka bai wa umarnin ba kuma a cewarsa babu yadda za a yi laifin wani ya shafe,
Ya kara da cewa ”Mun riga mun daukaka kara game da wannan hukunci, dan haka za mu jira domin ganin yadda shari’ar za ta kasance”
Amma ya ce duk da haka ya bayar da umarni a mayar da wannan motar alfarma ga mai ita tun a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekarar, tare da bayar da umarnin bin hanyar da ta dace wajen mayar da kudin naira miliyan 40 ga mai su.