Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa kudinsa $669,248 da N24.3m sun koma hannun gwamnatin tarayya.
Jaridar Daily Trust ta ce Abdulaziz Yari ya yi magana ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Mayowa Oluwabiyi, a ranar Lahadi, 31 ga watan Junairu, 2021.
Mayowa Oluwabiyi ya ce duk da Alkali mai shari’a, Ijeoma Ojukwu, ta bada umarni gwamnatin tarayya ta rike dukiyar mai gidansa, kotu ta ba shi kofa.
Oluwabiyi ya ce Ijeoma Ojukwu ta ba tsohon gwamnan kwanaki 14 domin ya yi wa kotu bayani mai gamsar wa da zai hana a karbe masa wadannan kudi.
A cewar Mayowa Oluwabiyi, tsohon gwamnan na Zamfara ya fara shirin daukaka shari’a a babban kotun daukaka kara, ya na kalubalantar hukuncin da aka yi.
Jawabin ya ce, Abdul’aziz Abubakar Yari, bai jin tsoron komai domin ya tabbatar da duk kamfanoni da kasuwancin da ya mallaka a gaban CCB.
Abdul’aziz Yari ya kuma bayyana cewa CCB ta tabbatar da kadarorin na sa bayan ya zama gwamna.
Yari ya yi mulki a jihar Zamfara tsakanin 2011 da 2019. Jagoran na APC ya yi kira ga jama’a su jira a karkare shari’a kafin su zartar masa da hukunci.