Zamu Rage Farashin Data A Najeriya – Pantami

Mataimakin Shugaban zartarwa, na Hukumar Sadarwa ta Najeriya, Umar Danbatta, ya bayyana cewa Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki da karkashin jagorancin Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami, na shirin rage farashin data daga N1,000 zuwa N390 a kowace gigabyte.

Da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar, Mista Danbatta ya bayyana cewa wani bangare na shirin shi ne sabon tsarin watsa shirye-shiryen harkokin sadarwa na kasa baki daya na shekara ta 2020-2025, wanda ya ce dole ne Najeriya ta samar da hanyoyin kafafen sadarwa ta hanyar sadarwa, don ta mamaye kusan dukkan sassan kasar sannan kuma ta samar da kayayyakin more rayuwa tare da samar tsarin sadarwa mai karfi 4G, a dukkanin fadin kasar.

A cewarsa, an dora wa ma’aikatar alhakin fito da tsarin tattalin arziki na zamani da dabaru, inda ya kara da cewa duk kokarin da aka yi an yi shi ne don dawo da kudin data zuwa N390 sabanin N1,000 da kamfanin sadarwa na Mobile, suke chajin al’ummar kasar.

Related posts

Leave a Comment