Zamu Kammala Da Boko Haram A Ƙarshen Wannan Shekarar – Sojin Sama

Rundunar sojojin sama ta Nijeriya ta sa wa dakarunta wa’adin wata shida su murkushe kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabas.

A jawabinsa ga sojojin Operation Lafiya Dole a Maiduguri ranar Asabar, Shugaban Rundunar, Sadique Abubakar ya ce gwamnati na yin abin da ya dace ga Rundunar kuma jiragen sintiri da aka kai gyara sun dawo daga Jamus inda aka kara musu kaimi domin taimaka wa yaki da Boko Haram.

Don haka, “Ku kara dagewa domin ina so kafin karshen shekarar nan ko zuwa karshenta mu kammala wannan yakin, saboda haka ku dage wajen ganin tabbatuwar haka, mu kuma za mu ci gaba da taimaka muku”, inji shi.

Da yake ba da tabbacin taimakon sojoji da duk abin da suke bukata, Saique ya ce an kusa shigo da jiragen yaki daga Amurka kuma nan kusa za a tura wadanda za a horas a kansu, “Don haka ku ci gaba da kokari, amma dole sai kokarin ya gamsar”, wajen tabbatar da tsaro a Arewa ta Gabas.

Ya yaba wa kokarin sojojin wajen yakar kungiyar Boko Haram a yankin, da kuma irin hadin kan da ke tsakanin rundunar da sauran rundunonin tsaro a aikin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply