Zamu Ƙauracewa Zaɓen 2023 Muddin Ba A Sauya Fasalin Najeriya Ba- Yarbawa

Shugabannin kungiyoyin Yarbawa a Najeriya sun yi barazanar kauracewa zabukan kasar na shekarar 2023, muddin aka ki amsa bukatarsu ta sauya fasalin tsarin mulkin kasar wato ‘Restructuring’ a turance.

Kungiyoyin Yarbawan sun sha alwashin ne cikin takardar bayan taron da suka fitar, inda suka ce sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya ne kadai zai ceto kasar daga cikin mawuyacin halin da ta fada, musamman ta fuskokin tsaro da kuma tattalin arziki.

Shugabanin da suka halarci taron hadin gwiwar sun hada da jagoran kungiyar Afenifere pa Reuben Fashoranti, da farfesa Banji Akintoye shugaban kungiyar Yoruba World Congress sai kuma tsohon gwamnan jihar Ondo Dakta Olusegun Mimiko.

Gamayyar kungiyoyin Yarbawan sun kuma koka kan rashin daidaito wajen raba mukamai da gwamnatin Najeriya ke yi, karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Labarai Makamanta

Leave a Reply