Zamfara Za Ta Fara Sayar Da Zinare A Ƙasashen Waje

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana yadda gwamnatinsa ta tanadi zinari mai kimar Naira Biliyan 5 ga abokan kasuwancinsu na kasar waje.

Zailani Bappa, mai bai wa gwamnan shawara akan yada labarai, ya bayyana hakan ga manema labarai a wata takarda a Gusau, babban birnin jihar.

Matawalle ya bayyana yadda dama yake da yarjejeniyar sayar wa wasu abokan kasuwancinsu dunkulen zinare na Naira biliyan 5 da dadewa.

Matawalle ya sanar da yadda yanzu haka suka siya kilograms 31 na zinare a wurin masu hako zinare daga kasa a jihar. A cewarsa, wannan dama ce da zasu bunkasa kudin shigar jihar Zamfara.

“Muna samun danyen zinaren ne a hannun masu hako zinare daga kasa. Muna wannan kokarin ne don tabbatar da cewa ‘yan jihar Zamfara sun amfana da ma’adanan jihar,” a cewarsa.

Gwamnan ya ce jihar zata cigaba da adana zinaren a bankuna, kuma ya tabbatar da cewa ba zai rintsa ba har sai jihar Zamfara ta bunkasa kuma ta kara kima a idon duniya.

“Matsalar da ake samu ita ce yadda imasu hako zinare ke hakowa kuma su fitar dashi kasar waje ba tare da wasu ‘yan jihar sun amfana ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply