Zamfara: Za A Kashe Miliyan 400 A Tallafin Karatun Dalibai

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da fitar da ku?i har naira miliyan 400 domin biyan ?alibai ‘yan asalin jihar tallafin karatu na zangon shekarar 2020/2021.

Tallafin ya shafi ?alibai ‘yan asalin jihar ta Zamfara dake karatu a cikin jihar da ma wa?anda ke karatu a wasu makarantun ?asar nan.

Wannan na daga cikin wani jawabi dake ?auke da sa hannun Yusuf Idris, Daraktan ya?a labaran gwamnan, wanda aka rarraba ga manema labarai a Gusau babban birnin Jihar.

Ya ?ara da cewar ?arkashin zangon karatu na 2020/2021, gwamnan ya amince a fitar da miliyan 186.6 don biyan ?aliban likitanci ‘yan asalin jihar da a yanzun suka shiga shekara ta biyu a karatunsu a ?asar Sudan.

Hakanan kuma Matawalle ya amince a fidda ku?i miliyan 24.5 don biyan ?alibai 25 da gwamnatin ke ?aukar nauyi a ?asar Indiya. Kuma ya amince da fitar da miliyan 56.4 ga ?ali?an dake karatu a Cypros.

A cewar daraktan ya?a labaran gwamnan: “Bayan gano gaskiyar lamarin bashin da ?aliban jihar ke bin gwamnati na tallafinsu a jami’ar Al-hikmah Ilorin, jihar Kwara da jami’ar Crescent dake Abeoukuta, jihar Ogun, gwamnan ya bada umarnin fitar da Naira miliyan 70.”

Gwamnan ya kuma amince da biyan miliyan 19 ga ?aliban dake karatun lauya na zangon karatun da ya gabata, 2019/2020. Ya ?ara da cewa gwamna Matawalle ya bada umarnin fara tantance ?alibai ‘yan asalin jihar dake karatu a makarantun gaba da sakandire a sassa daban-daban na ?asar nan.

Related posts

Leave a Comment