Daruruwan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Zamfara a ranar Lahadi sun tsinkayi hedkwatar ‘yan sandan jihar da ke Gusau, inda suka mika bukatarsu ta sakin shugabansu, Abu Dan-Tabawa da sauransu.
An kama Dan-Tabawa sakamakon ganinsa da aka yi dumu-dumu yana taro da ‘yan bindigar daji, kamar yadda hadimin gwamnan jihar Zamfara, Zailani Baffa ya sanar.
Masu zanga-zangar sun bayyana dauke da takardu kala-kala inda suke zargin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usman Nagogo da saka siyasa a lamarinsa ta yadda yake cafke ‘yan jam’iyyar daya bayan daya a jihar.
A yammacin ranar Asabar ‘yan sandan jihar suka damke Dan-Tabawa, wani makusancin tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, a gidan sa da ke Gusau bayan zarginsa da ake da zagon kasa ga tsaro.
Daya daga cikin masu zanga-zangar ya zargi kwamishinan ‘yan sandan da zama daraktan yakin zaben jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar.
“CP Nagogo ne shugaban tsari na PDP a jihar Zamfara,” ya rubuta a takardar da yake rike da ita.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, ya ce kama Dan-Tabawa da wasu mutum 17 da jami’an tsaro suka yi a ranar Asabar bashi da alaka da siyasa. Kakakin rundunar ‘yan sandan, Muhammad Shehu, a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, cewa an kama shi ne saboda zagon kasa ga tsaro da ake zarginsa da yi a jihar.