Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta samu nasarar daƙile hare-haren ‘yan bindiga a faɗin ƙananan hukumomin jihar guda hudu, tare da kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu, ya fitar ya ce ‘yan bindigar sun yi ƙoƙarin kai hare-hare a wasu ƙauyuka da ke ƙananan hukumomin Maru, da Bungudu, da Tsafe da kuma ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Ya ce jami’ansu sun samu nasarar daƙile hare-haren ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

SP Mohammed Shehu, ya ƙara da cewa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan bindigar na shirin ƙaddamar da hare-hare tare da mutane a ƙauyukan da ke wanɗannan ƙananan hukumomi

Labarai Makamanta

Leave a Reply