Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Bazama Neman Daliban Da Aka Sace


Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta baza jami’anta cikin daji domin ceto daliban makarantar gwamnati ta Kaya ta jeka ka dawo a yankin Maradun.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Mohammed Shehu ya fitar ya tabbatar da cewa dalibai 73 ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su daga makarantar.

Ya ce ‘yan bindiga da dama ne suka abka makarantar suka saci daliban.

Wannan na zuwa bayan gwamnati ta karbi daliban kwalejin noma da lafiyar dabbobi ta Bakura da aka kubutar bayan sun shafe kwanaki a hannun ‘yan bindiga.

Labarai Makamanta

Leave a Reply