Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace ‘ya’yan tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Zamfara – Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce, ‘yan bindigar sun shiga gidan tsohon kamishinan a Gamji da ke karamar hukumar Bakura wurin karfe 4:30 – Ya shawarci mazauna jihar da su kiyaye shigewa ‘yan bindigar a yayin da suka kai hari, su kai rahoto wurin ‘yan sanda ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘ya’yan tsohon kwamishina a jihar Zamfara, Bello Dankande, da wasu mutum biyu da suka hada da jami’an NSCDC. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya sanar da hakan a wata takardar da ya bai wa manema labarai a Gusau.
Ya ce an kashe mutum daya kuma wani ya ji miyagun raunika. Ya ce lamarin ya faru ne a gidan tsohon kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran masarautun da ke Gamji a karamar hukumar Bakura ta jihar a ranar Talata. Da duminsa: ‘Yan bindiga sun sace ‘ya’yan tsohon kwamishina a Zamfara.
‘Yan sanda sun damkesu “Wurin karfe 4:30 na asuba, ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kutsa gidan tsohon kwamishinan kananan hukumomi inda suka yi garkuwa da ‘ya’yansa biyu tare da jami’an NSCDC biyu da ke gadin gidan. “Sun harbe mutum daya yayin da wata mata ta samu miyagun raunika,” yace. Shehu ya ce rundunar ta tura jami’anta don nemowa tare da ceto wadanda aka sace, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. “Rundunar tana sake tabbatarwa da tsohon kwamishinan da dukkan jama’ar jihar cewa, za ta yi duk abinda za ta iya wurin ceto wadanda aka sace.
“Rundunar tana kira ga jama’a da su guji yin gaba da gaba da ‘yan bindiga a yayin da suka kawo hari. A maimakon hakan, su kai wa ‘yan sanda ko wasu jami’an tsaro rahoto,” ya kara da cewa. Kamar yadda yace, komai ya koma daidai a yankin kuma rundunar za ta sanar da jama’a a kan kowanne ci gaba da aka samu. Ba tun yau ba matsalar tsaro ta yi katutu a yankin arewa maso yamma na kasar nan.