Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Sallar Asubah

‘Yan bindiga sun kai hari Masallaci a lokacin da mutane ke shirin Sallar Asuba a kauyen Tazame da ke ?aramar hukumar Bungudu a Zamfara Rahotanni sun nuna cewa ?an bindigar sun kashe ladan da ?aninsa, sun yi awon gaba da mutane da dama ran Talata da safe

Kakakin rundunar ?an sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya ce sun tura karin jami’ai zuws garin domin dawo zaman lafiya

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa mazaunar kauyen ne a lokacin Sallar Asuba.

?an bindigar sun shiga kauyen suka kashe mutum biyu, ladanin Masallaci da kuma ?aninsa,” in ji shi. Ya kara da cewa maharan sun kuma harbi limamin masallacin wanda ya samu karaya a kafarsa tare da yin awon gaba da mutum kusan 10.

Wane mataki ?an sanda suka ?auka?

Jami’in hul?a da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce maharan sun kashe mutane biyu, sun sace wasu da dama. Ya ce rundunar ta tura karin jami’an ?an sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya tare da tabbatar da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

“Lamarin ya faru ne da safiyar Talata, maharan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama.”

Har yanzu ba mu tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba amma rundunar ?an sanda ta tura jami’anta yankin domin dawo da zaman lafiya. “Haka nan kuma muna ci gaba da ?o?arin ceto wa?anda maharan suka sace a harin.”
ASP Yazid Abubakar.

Related posts

Leave a Comment