Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 15 A Masallaci

Akalla mutum 15 ne suka mutu wasu kuma da dama suka jikkata a wani harin aka kai a wani masallaci dake jihar Zamfara mai fama da ƙalubalen rashin tsaro.

Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Ruwan Jema da ke yankin karamar hukumar Bukkuyum a jihar, inda ‘yan bindigar a kan babura suka nufi masallacin a yammacin ranar Juma’a suka fara harbi kan-mai-uwa da wabi.

Harin na zuwa ne makonni uku bayan da aka sace wasu masallata a masallacin Zugu na karamar hukumar.

A watan Yuli ma ‘yan bindigar sun kai hari a yankin tare da sace mutane da dama domin karbar kudin fansa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply