Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewar ‘yan ta’adda masu Garukwa da mutane sun shiga garin Kanoma dake karamar hukumar Maru ta jahar Zamfara a jiya juma’a dai dai lokacin da ake gabatar da sallar juma’a suka tafi da mutane 30 cikin har da Limamin garin na Kanoma.
Lamarin satar jama’a a yankin Arewacin Najeriya na ?ara ?aukar sabon salo, inda a kusan kullum ‘yan Bindiga ke kai farmaki akan jama’a su kashe na kashewa su kama na kamawa sannan su nemi ku?a?en fansa.
Gwamnatocin Jihohin Zamfara da Katsina inda Bala’in ‘yan Bindigar ya fi tu’azzara sun ?auki matakai a baya na yin sulhu da ‘yan Bindiga amma bu?ata ba ta biya ba, maimakon biyan bu?ata sai abubuwa suka ?ara dagulewa.
Hakika akwai tashin hankali ace irin taron ranar juma’a dan ta’adda ya ratsa masallacin juma’a ya tafi da Limami da sauran jama’a.
Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i.