Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Mutane 9 yan gida daya a kauyen Jangeme da ke Gusau a jihar Zamfara sun mutu, bayan cin tuwo mai guda.
Wani dan uwa ga iyalan Abdullahi Bello ya shaida wa Daily Trust cewa yaran sun mutu ne bayan cin tuwon dawar da wata yar uwarsu da ta je ziyara gidan ta yi.
‘’Babu wanda ya lura cewa garin dawar da ta yi girkin da shi ya gurbace sakamakon mutuwar bera a ciki, a haka ta dafa abinci da shi, ‘yan awanni kadan bayan sun ci daya daga cikinsu ya mutu’’.
Ya kara da cewa ‘’Da ganin haka sai suka kwashi sauran yaran zuwa asibitin Gusau inda biyu daga cikinsu ma suka mutu’’.
Yace lokacin da suka je makabarta don binne wadanda suka mutum sai aka sake kiran su daga gida aka shaida musu cewa uku sun kara mutuwa ciki har da kanwarsa da ta dafa musu abincin.
Gaba ɗaya dai yara takwas da mahaifiyarsu ne suka rasa ransu sanadiyyar kaddarar.