Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar jama’a sun dinga martani kan rahoton dake bayyana cewa gagararren ‘dan bindiga Bello Turji, wanda ya saba kashewa da garkuwa da jama’a a Sokoto da Zamfara ya tuba.
Idan za a tuna, a watan Disamban 2021, shugaban ‘yan bindigan ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Bello Matawalle da Sarkin Shinkafi kan yana so a tsagaita da ruwan wuta.
A yayin jawabi a wani taro a Gusau a ranar Lahadi, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji ya tuba kuma ya rungumi matakan zaman lafiya na gwamnatin jihar.
Nasiha yace Turji ya tuba kuma hakan ya dawo da zaman lafiya a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi a jihar.
“Turji yanzu halaka ‘yan bindigan da basu tuba yake ba, masu addabar jama’a a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a jihar”.