Zamfara: Sun Yi Nasarar Ƙwato Shanu 121 A Hannun ‘Yan Bindiga

Rundunar Sojin kasa ta Nijeriya sashin Ofureshion Hadarin Daji tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama na Nijeriya sashin Ofureshion Sahel ta samu nasara akan wasu manyan ‘an bindiaga, tare da ceto shanu daga hannun ƴan bindiga dake Dajin Zamfara da Katsina.

Zaratan sojojin sun samu nasarar kama wasu mutum biyar da ake tuhuma cewa ‘yan bindiga ne da shanu da tumaki guda 17 a kasuwar Maru na jihar Zamfara, bayan rundunan sojojin ta cigaba da bincike daga ƙarshe ta gano cewa ƴan bindigan ne, kuma sun sato shanun ne daga kauyen Gibiya.

An samu karbo shanu 121 da tumaki 37 daga hannun ƴan bindigan in da aka mika dabbobin ga masu su a garin Tsafe dake jihar Zamfara.

Rundunan soji ta samu nasarar kama wasu a kauyen Jagawar Malamai a ƙaramar hukumar Danmusa dake jahar Katsina. An samu nasarar kama ƴan binga hudu tare da bindiga kirar Ak47 da mashuna guda 21 a inda suke zaune a dajin, wanda sojojjn suka lalata kayan ƴan bindigan gaba daya da kashe wasu ‘yan bindiga bayan sun yi musayar wuta tsakaninsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply