Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Alhaji Ahmad Sani Kaura ya riga mu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa, ya yanki jiki ya fadi ne a ranar Laraba a Gusau yayin wani taron zaman lafiya da aka gudanar da majalisar Ulama kan zaben 2023 mai zuwa.
Da yake ƙarin haske dangane da rashin da aka yi wani Jigon PDP a jihar, Aminu Umar ya bayyana cewa, Kaura ya kasance ba shi da lafiya, kuma bai murmure ba lokacin da ya halarci wannan zama.
Rasuwarsa na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da aka zabe shi ya zama shugaban PDP a jihar ta Zamfara.
Idan mai karatu bai manta ba, an zabi Kaura ne da mataimakinsa a watan Satumban bana domin ci gaba da kula da lamurran PDP na tsawon shekaru uku a Zamfara.