Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar zamfara ta ceto mutum 27 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ?aramar Hukumar Anka ta jihar.
Kakakin ‘yan sanda na Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a garuruwan Akawa, da Gwashi, da Tungar Rogo da kuma wasu ?auyuka, inda aka kai su sansanoni a Gando/Bagega da ke dajin Sunka a ?ananan hukumomin Anka da Bukuyum.
Ya ce an yi nasarar ceto mutanen sakamakon rahoton da suka samu cewa ‘yan fashin daji sun kai wa garuruwan hari, amma sai da suka shafe mako ?aya a hannun maharan.
“Jim ka?an bayan samun rahoton, Kwamashinan ‘Yan Sanda Kolo Yusuf ya aika da ?arin ‘yan sanda zuwa ofishinsu na Anka da Bukuyum da kuma ‘yan sa-kai don ceto mutanen,” a cewar sanarwar da SP Shehu ya fitar.