Jam’iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da barkewa wanda har hakan ya kai ga kotun koli dake Abuja, ta shigo ciki domin shawo kan rikicin.
Sakamakon taron Jam’iyyar APC da aka yi a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, wanda aka nada shugabannin Jam’iyyar na jihar Zamfara ya jawo rikici, kamar yadda bangaren da Sanata Marafa ke jagoranta ke ganin cewa kotun daukaka kara ta yanke hukuncin da basu gamsu da shi ba, zasu kai kara kotun koli.
Bangare daya na jam’iyyar, wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta sun ce za su daukaka kara zuwa kotun koli akan hukuncin da kotun daukaka kara ta Sokoto tayi akan taron jam’iyyar.
Kamar yadda kotun daukaka kara ta Sokoto ta tabbatar kuma ta gamsu da hukuncin da taron nadin shugabannin jam’iyyar da akayi a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, wadda Alhaji Lawal Liman ya jagoranta.
Kotun daukaka karar ta Sokoto ta yanke hukuncin da babbar Kotun Zamfara ta yi, wacce ta rushe duk nadin da taron yayi.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Bello Bakyasuwa yace bangaren da Marafa ke jagoranta basu amince da hukuncin kotun daukaka karar ba. Yace don kawai tsohon Gwamna Abdulaziz Abubakar Yari na jagorantar dayan bangaren baya nufin sune za su nada shugabannin Jam’iyyar.
Ya kuma zargi shugabannin Jam’iyyar APC na kasa akan mara wa bangare daya baya, da nuna son kai wurin hukunci. Yace bangarensu na bukatar hukuncin gaskiya da gaskiya.