Wasu masu kishin al’umma sun gabatar da koke dangane da farmakin da wasu da ake zaton ‘yan bangar siyasa ne su ka kai wa ‘yan jam’iyyar PDP yayin da su ke gudanar da babban taron su a karkashin jagorancin mataimakain gwamnan jihar Zamfara Mahadi Aliyu Gusau a garin Gusau na jihar Zamfa.
A cikin wata takardar koke da su ka aike wa shugaban Hukumar Kula da Harkokin ‘yan sanda da Ministan ‘yan sandan Nijeriya dauke sa da hannun dan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam Muhammad Lawal Gusa, sun bukaci a gudanar da kwakkwaran bincike domin gano gaskiya musabbabin farmakin.
Sanarwar ta kara da cewa, babban abin takaicin shi ne, lamarin ya faru ne yayin da kwamishinan ‘yan sanda na jihar yay i tafiya ba tare da an samar da kwakkaran tanadi ba duk kuwa da an sanar da su game da taron.
Takardar korafin dai, ta na dauke da bukatar a gudanar da bincike dangane da ta’adin da aka yi wa mahalarta taron, kuma har yanzu ba a sanar da an kama kowa ba.
Idan dai ba a manta ba, Gwamna Matawalle da magoya bayan sa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yayin da mataimakin sa Mahadi Aliyu Gusau da Magoya bayan sa su ka cigaba da kasancewa a cikin jam’iyyar PDP.