Gwamnatin jihar Zamfara ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Muhammadu Bello Matawallen Maradun, ta bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana dake jihar gaba daya, ba tare da wani ?ata lokaci ba.
Gwamna Bello Matawalle ya ?auki matakin yin hakan ne sakamakon sace ?aruruwan dalibai Mata na makarantar sakandaren GGSS Jangebe da aka sace a karamar hukumar Talata Mafara dake jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar da yammacin Juma’a a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara dangane da iftila’in.
Matawalle ya jaddada cewa zai cigaba da shirin yin afuwa ga ‘yan bindiga domin su ajiye makamansu. A cewarsa, harsashi ko da guda daya ne a hannun dan bindiga na da hadari ga al’ummar jihar.
“Yanzu haka, an tura jirage masu saukar angulu na ‘yan sanda domin ceton yaran. Za’a sanar da iyayen yara da jama’a halin da ake ciki game da wannan yunkuri da ake yi inji Matawalle.
“Yayinda muke kokarin karfafa tsaro a makarantun mu, na bada umurnin kulle dukkan makarantun sakandare na kwana dake fadin jihar.”