Zamfara: Matawalle Ya Bada Umarnin Kai ‘Yan Matan Da ‘Yan Bindiga Suka Sako Asibiti

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Mohammed Bello Matawalle ya bayar da umarnin kai ‘yan matan nan biyar -da aka sako daga hannun ‘yan bindiga – asibiti domin a duba lafiyarsu na ‘yan kwanaki kafin su koma cikin iyalansu.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai Zailani Bappa ya sanya wa hannu, ya ce maitaimakin babban sifeton ‘yan sanda mai lura da shiyya ta 10, AIG Bello Sani Deljan, tare da kwamishin ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ne suka jagoranci yaran biyar zuwa fadar gwamnan, bayan kubutar da su daga hannun’yan bidigar.

‘Yan matan biyar sun kwashe wata biyar a hannun ‘yan bindigar.

Gwamna Matawalle ya yaba wa jami’an tsaron da ke aiki a jihar, tare da kiran su kara kaimi wajen kawo karshen ayyukan ‘yan fashin daji da ke addabar jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply