Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa mai girma gwamna Bello Matawallen Maradun na shirye shiryen komawa jam’iyya mai mulki ta APC nan bada jimawa ba.
Tun a watannin baya ne aka ri?a ya?a jita-jita game da sauya shekar Gwamna Matawalle, wanda ya zama gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP, bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani na APC a Zamfara.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, a shekarar da ta gabata ya bayyana cewa shirye-shirye na gudana kan komawar Matawalle APC.
A cewar wata majiya, rikicin da ya dabaibaye APC a jihar na daya daga cikin abubuwan da suka kawo tsaiko ga ficewar gwamnan daga jam’iyyar PDP.
An ruwaito cewa ana iya kulla yarjejeniyar a ranar Talata, 6 ga Afrilu lokacin da tawagar gwamnatin tarayya za ta ziyarci Zamfara don yi wa gwamnan jaje kan gobarar da ta faru a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya kwashe tsawon watanni yana tattaunawa da akalla gwamnoni biyu na jam’iyyar ta APC.