Rahotanni dake shigo mana yanzu daga birnin Gusau na jihar Zamfara na bayyana rasuwan Hon. Muhammad G. Ahmed (Walin Jangeru), ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Shinkafi.
Ya rasu awanni da sauya sheƙa zuwa APC daga jam’iyyar PDP. Yana daga cikin tawagar ƴan majalisun da ta bi gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle suka fice daga PDP.
An bayyana cewa, har zuwa daren jiya yana tare da jama’a a gidan gwamnatin jihar dake birnin Gusau wurin bikin sauya jam’iyyar su