Zamfara: Bello Turji Ya Kalubalanci Soji Kan Gaza Kashe Shi

Labarin dake shigo mana daga jihar Zamfara na bayyana cewar Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, shahararren ‘dan ta’adda ne kuma shugaban ‘yan bindiga dake addabar jihohin Zamfara, Sokoto da Niger yace gwamnatin Najeriya bata da ra’ayin kawo karshen ta’addanci saboda wasu jami’an suna amfana daga shi.

Turji ya sanar da hakan matsayin martani ga luguden wutan da sojoji suke yi a gidansa kuma ya zargi gwamnatin da tunzurasu ta yadda har zasu karya yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi da mazauna yankin.

Bello Turji a farkon shekarar nan ya jagoranci ‘yan kungiyarsa inda suka yi wa Zamfarawa kusan 200 kisan gilla har da mata da kananan yara. A ranar 21 ga watan Augustan wannan shekarar, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Muhammad Hassan Nasiha, ya sanar da cewa Turji ya rungumi zaman lafiya.

Amma a ranar 18 ga watan Satumban, ya sha da kyar yayin da dakarun sojin saman Najeriya suka yi masa luguden wuta a gidansa dake kauyen Fakai na karamar hukumar Shinkafi ta jihar, lamarin da yayi sanadiyyar kisan mayakansa 12 da ‘yan uwa.

Hedkwatar tsaro ta kasa a ranar 14 ga watan Nuwamba ta ayyana nemansa da wasu ‘yan ta’adda 18 ruwa jallo inda ta saka kyautar N5 miliyan kan kowannensu.

A yayin martani kan luguden wutan da aka yi a gidansa, shugaban ‘yan bindigan ya zargin gwamnatin da karya alkawarin zaman lafiya da suka yi tare da baiwa jama’a kariya a yankin Shinkafi.

A yayin zantawa da wani gidan talabijin na Hausa Turji ya bayyana fushinsa kan ruwan wutan da ake yi a gidansa tare da halaka mutane marasa laifi bayan ya amince da jami’an gwamnati da shugabannin al’umma cewa zai bar ta’addanci.

“Ina mamaki idan da gaske gwmanati tana son halaka ni. Ina tunanin so suke su tunzura ni in karya alkawarin da na dauka na cewa na daina kisa. Idan har zasu iya ganin gidana, me zai sai ba zasu ganni su halaka ni ba, saboda mintuna kadan na bar gidan kafin su yi ruwan wutan.

“Jama’a ya kamata su san makiyansu tun daga farko. Gwamnati tunzura mu take yi ta yadda zamu dauka fansa a kan talakawa. “Gwamnati yaudarar jama’a take kan cewa tana son kawo karshen ta’addanci duk da cewa su ne ke hura wutar ta’addanci kuma suke mora daga ta’addancin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply