Zamfara: Ba Zamu Fasa Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga Ba – Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce sulhu ne kadai hanyar tabbatar da dawamammen zaman lafiya daga matsalar ‘yan fashin daji da suka addabi yankin arewacin maso yammacin kasar.

A cikin wata sanarwa, Gwamna Bello Matawalle ya ce shi bai yi nadamar yin sulhun da ya yi da ‘yan bindiga saboda yadda hakan ya taimaka wajen raguwar hare-hare a jiharsa.

Mai magana da yawun gwamnan Zailani Bappa ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Zamfara ta ga alfanun sulhun da ta yi da ‘yan bindiga masu fashin daji inda ya ce anb karbimakamai sama da dubu daya daga ‘yan bindigar.

“An samun zaman lafiyar da ya kai ga dawo da cin kasuwannin mako mako da aka daina kuma aka dawo bin hanyoyin da a baya suka gagara,” inji shi.
Amma a watan da ya gabata ne gwamnatin Katsina mai makwabtaka da Zamfara ta ce ta yi da na sanin yin sulhun da ‘yan bindigar inda gwamnatin Jihar Aminu Bello Masara ya shaidawa BBC cewa gwamnatinsa ba za ta kara yin sulhu da ‘yan bindigar ba saboda yadda suke ci gaba da kai hare-hare.
Jihar Zamfara: Ana zaman ɗar-ɗar bayan ‘yan fashi sun kashe mutum 21
Gazawar Gwamna Matawalle ta fara bayyana a Zamfara – Yari
Bello Matawalle: Abdulaziz Yari ne ummul aba’isin rikicin Zamfara
A nata bangaren gwamnatin jihar Zamfara ta ce sai idan jihohin da ke makwabta da zamfara sun rungumi irin sulhun da gwamna Matawalle ya yi za a samu dorewar zaman lafiya.
“Ko an yi sasanci ba zai dore ba, idan ba a hade kai tsakanin jihohin da matsalar ta shafa ba,” inji Zailani Baffa mai magana da yawun gwamna Matawalle.
Ya kara da cewa wasu tsiraru ne da ba su amince da sulhu ba suke kai hare-hare a Zamfara amma kusan kashi 80 cikin dari na ‘yan fashin dajin sun rungumin sulhun da gwamnati.

Gwamnatin ta Zamfara ta ce ta sake bullo da wani tsari na tabbatar da sasanci inda ta ce duk wadanda ba su amince da sulhun ba za a barsu da jami’an tsaro.
Wasu na ganin matakin gwamnan na yin sulhu ba shi da amfani ganin cewa ‘yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Zamfara.
Ko a watan jiya, Mazauna garin Ruwan Tofa cikin ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara sun auka cikin tashin hankali bayan ‘yan fashin daji sun yi wa yankinsu tsinke.
Bayanai sun nuna cewa akalla mutum 21 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin ‘yan fashin daji a garin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply