Zamfara: Ana Cigaba Da Kidaya Gawarwakin Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun halaka fiye da mutane 30, sannan sun yi garkuwa da wasu wadanda yawanci mata ne sakamakon hare-hare daban-daban a ranar Juma’a cikin fa?in Jihar.

An ruwaito ‘Yan bindigar sun kai harin ne kauyen Nasarawar Mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina da ke karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Bakura.

Tun a shekarar 2021 hare-hare suka yawaita a yankin. Majiyoyi daban-daban sun shaida cewa sun kai harin Nasarawar Mai Fara ne saboda mazauna yankin sun gaza biyan harajin Naira miliyan 40 da suka kallafa musu. Wani shu’umin dan bindiga, Ada Aleru ne ya ke jagorantar ta’addanci a yankin da wuraren Faskari da ke Jihar Katsina.

Abubakar Bala, mazaunin Tsafe ya ce sun kai harin da ya shafi fiye da mutane 20 wadanda suka rasa rayukansu a ranar Juma’a da yamma sun halaka babban limamin yankin.

A Bakura kuwa, wani ma’akacin asibiti, Masud Kyambarawa ya sanar da cewa sun halaka mutane uku a yankin ciki har da babban limamin yankin, Akilu Dan Malam.

“Jiya ina garin na ji ana harbe-harbe. Daga nan muka gudu wani kauye da ke makwabtaka da garin a Rabah, Jihar Sokoto gaskiya mummunan lamari ne.

“Musamman yara da mata sai gudu suke yi dajika don tsira. Alhamdulillah mun dawo lafiya amma mun ji labarin yadda mutane 3 suka rasu.”

A kauyen Yar Katsina da ke Bungudu kuwa, ‘yan bindiga sai da suka hana mutane zuwa sallar Juma’a. Yanzu haka dai an tsinci gawawwaki 10 na jama’a a kauyen Yar Katsina.

Abdul Balarabe, wani dan jarida da ke Gusau ya ce akalla mutane 10 ne suka rasu sakamakon harin amma har yanzu akwai wadanda ba a gani ba, akwai yuwuwar garkuwa da su aka yi. Bala ya kara da cewa: “An ga gawawwaki 10 kuma har yanzu akwai wadanda ba a gani ba.

Mazauna yankin sun ce ba su tabbatar ko garkuwa da su aka yi ba ko kuma boyewa su ka yi ba. ‘Yan bindiga sun shiga kauyen ne lokacin sallar Juma’a.” Bala ya koka akan hare-haren da ke kara yawa a titin Funtua zuwa Gusau.

Related posts

Leave a Comment