ZAMFARA: An Bankado Likitocin Bogi 199 Masu Albashi

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ya ce gwamnatin jihar ta gano sunayen likitocin bogi kimanin 199 waɗanda ake biyan albashi a jihar.

Gwamna matawalle na wannan jawabi ne ga taron manema labarai a shalkwatar ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar.

A cewar gwamnan yayin da gwamnatin jihar ke biyan likitoci 280 albashi a jihar a duk wata, ta gano cewa likitoci 81 ne kawai ke aiki a jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa tuni ya zanta da ƙungiyar kwadago ta ƙasa domin gano waɗanan, likitoci 199 da suka ƙwashe tsawon lokaci suna karɓar albashi alhalin ba sa yi wa gwamnatin jihar aiki.

Da kuma gano waɗanda ke da hannu a wannan cuwa-cuwa.

Matawalle ya ce an gano waɗannan sunaye ne sakamakon aikin tantance ma’aikata da gwamnatin jihar ke gudanarwa ƙarƙashin ofishin shugaban ma’aikata na jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply