Zamfara: An Bada Hutun Kwanaki 5 Domin Rijistar Zabe

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta ba ma’aikatan jihar hutun mako ?aya domin su yi rajistar katin za?e da ake gudanarwa yanzu haka a fa?in ?asar.

Matakin na ?unshe ne cikin wata sanarwa da Kwamashinan Ya?a Labarai na Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar a yau Asabar.

Ya ce Gwamna Bello Matawalle ya amince da ba da hutun ne daga Litinin, 20 zuwa 24 ga watan Yuni.

“Sakamakon wannan sanarwa, an umarci dukkan kwamashinoni da masu bai wa gwamna shawara da sakatarori da sauran ma’aikatan gwamnati da jami’an jam’iyyun siyasa da su saka ido kan yadda aikin rajistar ke tafiya,” a cewar kwamashinan.

?ungiyoyi da ‘yan gwagwarmaya a Najeriya na ci gaba da kira ga hukumar za?e ta ?asa INEC da ta tsawaita wa’adin yin rajistar, suna masu cewa mutane da dama ba su samu damar yi ba saboda ?arancin kayan aiki da kuma cunkoso.

INEC ta saka ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar ?arshe da za a rufe aikin rajistar.

Related posts

Leave a Comment