Akalla gidaje 110 ne ambaliyar ruwan ya shafa a garin Zagwanye karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, biyo bayan wata musiba ta ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Laraba.
Hakan yana kunshe cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a cikin Gusau, babban birnin jihar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai ba Gwamna Bello Matawalle shawarwari na musamman kan harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Fa’ika Ahmad.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da hukumar kula da yanayi NIMET ta yi hasashen za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana.