Zalunci Ne Ƙarin Farashin Mai A Yanzu -Atiku

Atiku Abubakar ya bayyana cewar babu wani dalilin kara farashin man fetur a halin kunci da talaka ce ciki na matsin tattalin arziki, ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce kamata ya yi ace litar mai ta sauko ganin yadda kasuwar danye mai ta Duniya ta yi kasa a wannan shekara.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce akwai badakala da rashin gaskiya a yadda ake biyan ‘yan kasuwa tallafin mai, ya ce wannan ya hana kasar nan cigaba.

A farkon watan Satumban nan sai aka ji cewa humumar PPMC ta bayyana karin farashin man fetur, ta bada umarni a rika bada sarin lita a kan N138 zuwa N156.

Wannan canjin farashi da aka samu ya jawo ana saida man fetur tsakanin N159 da N162 a gidajen mai.

Alhaji Atiku Abubakar ya fito ya yi magana game da lamarin, ya ce ya kamata ace kudin fetur ya yi kasa idan aka yi la’akari da abin da ake saida gangar danyen mai.

Atiku wanda sanannen ‘dan kasuwa ne ya jefawa gwamnatin tarayya tambaya a kan dalilin da ya sa fetur ya ke kara tsada, a lokacin da ya ke rage kudi a Amurka da Turai.

Atiku ya rubuta: “Ni ‘dan kasuwa ne. Ina kallon abubuwa ta madubin tattalin arziki. Tambayoyi na kishin amsoshi. Farashin danyen mai ya yi kasa daga inda ya ke a 2019.”

Labarai Makamanta