Kungiyar mabiya a?idar Shi’a a Najeriya wadda ake wa la?abi da (IMN) da karyata labarin cewa jagoran ?ungiyar Ibrahim Zakzaky ya mutu.
Jita-jitar mutuwar Zakzaky ta bazu a garin Kaduna ne a ‘yan kwanakin nan, inda hakan ya jefa tsoro a zukatan ‘yan Shi’a, sannan sauran jama’a suka shiga fargaba saboda tsoron abin da ka je ya dawo.
A zantawar da aka yi da wani ?an Shi’a mai suna Abdullahi Usman a Kaduna ya tabbatar da cewar jagoransu Zakzaky yana nan a raye bai mutu ba, kuma tabbas sai ya yi nasara a shari’ar da ke gudana tsakaninsu da gwamnatin Jihar Kaduna.
“Ban san daga inda mutane suka jiyo wannan jita-jitar ba, amma ina tabbatar maka cewa shugaban mu yana nan da ransa.
“Ba zai haifar wa gwamnati da mai ido ba idan shugaban mu ya mutu a hannun ta,” ya kara da cewa.