Zabena Ne Zai Share Wa Inyamurai Samun Zama Shugaban Kasa – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce shi tsani ne ga kabilar Igbo wajen fitar da shugaban kasar Najeriya daga cikinsu. Atiku, wanda ya yi magana a dandalin Alex Ekwueme, Akwa, a yayin taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Anambra, ya yi alkawarin taimakawa kabilar Igbo wajen fitar da shugaban kasa bayan wa’adinsa.

“Zan zama matattakalar tabbatar da kabilar Igbo sun samu shugaban kasa muddin kuka zabe ni a 2023.” “Zaku iya tabbatar da hakan, in kun lura wannan shi ne karo na uku da zan yi takara da dan kabilar Igbo a matsayin Mataimakina.” “Idan da gaske kuna son samar da shugaban kasa, to ku zabi Atiku/Okowa,”

Ya kuma yi alkawarin tabbatar da tashar gabar ruwan Onitsha ta fara aiki idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar zaɓe ta 2023.

Atiku, wanda ya kai wa Gwamna Chukwuma Soludo ziyarar ban girma a Awka, ya bayyana gwamnan jihar Anambra, a matsayin amintaccen abokinsa, wanda zai hada kai dashi dan ciyar da Najeriya gaba idan aka zabe shi a 2023. Ya ce dangantakarsa da Soludo ta wuce siyasar bangaranci, amma sun hadu a niyar yin gyare-gyare tare, dan bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

“Wannan ya wuce siyasar jam’iyya. Kamata ya yi a samu matsaya kan yadda za mu ci gaba, kuma ni ina daukar gwamna Soludo a matsayin wanda muke da zuciya daya ta bunkasa Nigeria”. “Duk da bambance-bambancen da ke tsakaninmu na siyasa, ya kamata a sami wasu muhimman dabi’u da ya kamata mu amince da su wajen ci gaban kasarmu.”

A nasa jawabin, Soludo ya ce ci gaban Najeriya ya kamata ya zama babban fifiko ga kowane dan siyasa ko dan takara. A cewarsa Najeriya ta fi kowace jam’iyya girma kuma burin gina kasa ya fi kowane dan siyasa girma. “A cikin wannan buri na gina Najeriya, Anambra da yankin Igbo su zama wata cibiya da za’a rinka kwakwayonta wajen bunkasa kasa da yanayin tattalin arziki”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply