Zaben 2023: Tarayyar Turai Za Ta Turo ‘Yan Sa Ido 100 Najeriya

?ungiyar tarayyar Turai ta ce za ta tura jami’anta 100 domin sanya ido a babban za?en Najeriya da ke tafe.

Shugaban kwamitin sanya ido kan za buka na ?ungiyar Barry Andrews ne ya bayyana haka a lokacin ?addamar da kwamitin ?ungiyar kan za?en Najeriya na 2023 ranar Litinin a Abuja babban birnin ?asar.

Mista Andrews ya ce ?ungiyar EU ta kafa kwamiti kan Za?en Najeriya ne bayan da ta samu gayyata daga Hukumar Za?e Mai Zaman Kanta ta Kasar (INEC.

Ya kuma ce tuni jami’an EU 11 suka fara aiki tun ranar 11 ga watan Janairu, a ?angarori daban-daban na shirye-shiryen za?en.

Ya ?ara da cewa wannan shi ne karo na bakwai da ?ungiyar ke sanya ido a za?ukan Najeriya.

Ya ci gaba da cewa jami’an ?ungiyar sun ?unshi ?wararru a fannin fasahar zamani kasancewa wannan shi ne karo na farko da Najeriya za ta gudanar da za?uka ta hanyar amfani da na’urorin da ke aiki da fasahar zamani, musamman domin tantance masu ka?a ?uri’a da kuma aika sakamakon za?e.

Related posts

Leave a Comment