Zaben 2023: Mu Jingine Kabilanci Mu Zabi Cancanta – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmai kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya shawarci ‘yan Najeriya game da zaben 2023, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su natsu a zabe mai zuwa, su zaɓi shugabanni masu kyawawan halaye.

Sultan ya yi wannan kira ne ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga mahalarta taron majalisar kula da albarkatun ruwa ta kasa (NCWR) a jihar Sakkwato.

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa babban zaɓe na ƙara matsowa kuma ‘yan Najeriya na bukatar su sa wayewa da basira wajen amfani da kuri’unsu. “Yan Najeriya na bukatar su yi tunani su ƙara nazari kan nazari kan wanda zasu jefa wa kuri’unsu, bai kamata mu duba Addini ko kabilanci kan kowaye zamu zaba ba, kishin Najeriya ne a farko.”

“Kasar mu ya kamata mu fifita a saman komai kuma kar mu sake mu zabi mutumin da zai ƙara lalata yanayin da muke fama a yanzu.” Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya ƙara da cewa idan har ana son Najeriya ta ci gaba, ya zama wajibi ‘yan kasa sun jingine batun Ƙabilanci a fuskanci zahiri.

Sarkin ya ci gaba da cewa: “Ƙasar mu tayi wa wasu kasashe da dama nisa a bangaren tsaro saboda haka ya kamata mu cigaba da goyon baya da yabon ƙasarmu da shugabanninmu domin su samu karsashin magance ƙalubalenmu.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply