Hukumar Za?e Mai Zaman Kanta ta ?asa INEC ta tsawaita wa’adin kar?ar katin za?e da a ke gudanawar a halin yanzu a fadin ?asar.
A wata sanarwa da kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin ya?a labarai da ilimantar da masu ka?a ?uri’a Festu Okoye ya fitar ranar Asabar ya ce hukumar ta ?ara wa’adin kar?ar katin za?en daga 29 ga watan Janairu zuwa biyar ga watan Fabrairu.
Sanarwar ta ?ara da cewa “Hukumar Za?e ta zauna a yau Asabar 28 ga watan Janairu kwana guda bayan ta gana da kwamishinoninta na jihohi 36 da Abuja, ta kuma yanke hukunci game da tarin matsalolin da aka gabatar mata , ciki har da batun yadda kar?ar katin ke gudana a ?ananan hukumomi 774 na fa?in ?asar”.
“Sakamakon rahotonnin tsaikon da aka samu na kar?ar katin za?en da kwamishinonin za?en na jihohi suka tattauna hukumar ta yanke hukuncin tsawaita wa’adin kar?ar katin zaben zuwa mako guda”.
Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar za?en ?asar ke sauya ranar rufe kar?ar katin za?en, wanda a baya ta saka ranar 12 ga watan Disamban 2022 kafin ta ?aga shi zuwa ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.
A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ne dai hukumar za?en ?asar za ta gudanar da za?en shugaban ?asa, da na ‘yan majalisun dokokin ?asar.