Zaben 2023: Gwamnoni Za Su Gana Da Buhari Kan Karancin Sabbin Kudi Da Fetur A Yau

Gwamnonin jam’iyya mai mulki ta APC sun shirya ganawa da shugaban ƙasa Buhari dangane da babban zaɓe dake tafe da matsalar rashin sabbin kudi da karancin fetur a faɗin ƙasar.

Gwamnonin sun koka dangane da yadda ƙarancin takardun kudi da matsalar man fetur suka jefa jama’ar kasar cikin mawuyacin hali wanda ya shafi harkar rayuwa gaba daya.

‘Yan Najeriya da dama sun koka dangane da halin ƙunci da suka shiga tun bayan shelanta sake fasalin Naira da kuma yanayin da suke ciki kan matsalar fetur lamarin da suke ganin zai iya haifar da kalubale a babban zaɓe dake tafe

Gwamnan Jíhar Kaduna Nasiru El-Rufa’i a ranar Laraba ya bayyana a tashar talabijin ta Channels inda ya kwarmata cewar lallai halin da ake ciki na batun sauya takardun kudi da karancin fetur wani yunkuri ne na zagon kasa da wasu shafaffu da mai a fadar shugaban ƙasa ke yi wa ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu.

Wata majiya ta bayyana cewar Gwamnonin za su bayyana damuwarsu ga shugaban ƙasa kan yadda waɗanda ya naɗa a muƙamai kuma makusanta ke aiki ga Jam’iyyar adawa da niyyar ganin APC ta faɗi a zabe, inda za su buƙaci daukar matakan da suka dace domin tsamar da “yan Najeriya shiga mawuyacin hali.

Sannan za su bukaci shugaban ƙasa da ya umarci Gwamnan Babban bankin Najeriya Emefiele ya yi garambawul ga batun sauyin takardun kuɗin, yadda za a samu tsawaita lokaci sosai domin amfanuwar jama’ar ƙasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply