Zabarmari – Da Gangan Sojoji Suka Bari Aka Yi Wa Manoma Yankan Rago – Salihu

Mazauna garin Zabarmari sun sanar da sojoji game da harin da aka kai masu amma babu abunda aka yi, kamar yadda suka bayyana a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba.

An ruwaito cewa wani mazaunin kauyen da ya tsira, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Abubakar Salihu, ya bayyana cewa sun hango hatsarin bayan sun kama wani dan Boko Haram sannan suka mika shi ga jami’an tsaro.

“Mun sanar da sojoji cewa Jama’armu sun gano yan Boko Haram da yawa amma babu abunda aka yi game da hakan.
“Ranar bakin ciki ne garemu a Zabarmari; da an dakile harin amma sojoi suka ki daukar mataki kan bayanan da muka basu,” in ji shi.

Wani manomin shinkafa, Mohammed Alhaji, da aka zanta dashi ya ce mutanen da aka kashe sun dukufa wajen girbe shinkafa lokacin da mayakan suka far masu sannan suka tattara su, kafin suka karkashe su ta hanyar yi musu yankan rago.

“Da gangan ne don tabbatar da ganin cewa bamu girbe albarkatun gonanmu ba. Muna bukatar gwamnatin tarayya ta taimake mu sannan ta kare mana rayukanmu,” in ji shi.

Ya tabbata cewa harin ya wakana ne a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, yayinda mayakan Boko Haram suka zagaye manoma a gonakinsu sannan suka yi masu yankan rago.

Gaba daya gawawwakin da aka samu a wuri guda bayan harin ya kasance 43. Gawawwakin da aka samo a wasu wuraren ya daga yawan mutanen da suka mutu zuwa 110.

Related posts

Leave a Comment