Za Mu Yi Keke Da Keke A Babban Zabe Dake Tafe – INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take game da zuwa zaɓen zagaye na biyu na shugaban ƙasar idan har ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba.

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban zaɓen ƙasar da ke tafe a Chatham House da ke birnin Landan a Birtaniya.

Ya ƙara da cewa a INEC ta yi shirin yiyuwar zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda take yi a zaɓuka uku da suka gabata.

Shugaban hukumar zaɓe ya kuma ce zaɓen ƙasar da za gudanar cikin wannan shekara zaɓe ne na matasan ƙasar.

Farfesa Yakubu ya kuma ce rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta nuna cewa matasa ne suka mamaye adadi mafi yawa na masu rajistar zaɓen.

Shugaban Hukumar ya ce ya ji daɗin yadda mutane suka fito domin karɓar katinan zaɓensu, yana mai cewa fiye da mutum 600,000 sun karɓi katinansu a jihar Legas kaɗai cikin watan da ya gabata.

Ya ƙara da cewa a yanzu adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya sun kai miliyan 93.4, kuma daga ciki miliyan 37 wato kashi 39 na rajistar zaɓen matasa ne ‘yan tsakanin shekara 19 zuwa 34.

Ya kuma tunasar da maharta taron cewa hukumar za ta tsayar da rabar da katin zaɓen daga ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.

2- Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Rijistar Sabuwar Ƙungiyar Malaman Jami’a

Gwamnatin tarayyar ta kammala yi wa sabuwar ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasar mai suna ‘Congress of University Academics’ (CONUA).

Ministan ƙwadago na ƙasar Dakta Chris Ngige, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim ƙadan bayan tattaunawar sirri da shugabannin sabuwar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Niyi sunmonu.

Ministan ya kuma gargaɗi sabuwar ƙungiyar da cewa kada ta ɗauki hanyar da takwararta ta ‘Academic Staff Union of Universities’ (ASUU). ta bi

Ya umarci ƙungiyar da ta yi aiki a duka jami’o’in ƙasar ba tare da fargabar kowa ba, yana mai cewa gwamnati ta ɗauki matakin kawar da ‘katutun’ da ASUU ta yi tare da lalata tsarin jami’o’in ƙasar.

A shekarar da ta gabata ne dai aka ƙirƙiri sabuwar ƙungiyar lokacin da kan malaman jami’o’in ƙasar ya rabu kan yajin aikin da ƙungiyar ASUU ta share kusan wata takwas tana gudanarwa a faɗin ƙasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply